Daga Abubakar Sale Yakub

Talaka ya kwana ya tashi bai ci ba, sabo da karfin hali haka zai sake fita nema a taskar Allah.
Yayin da wanga wadan cha nan ka suke haka Rami su binne na Gwamna masu gida rana (Kudi) Dan gudun talauci.
Wannan rayuwa ta munana amma dai nasan tabbas babu wanda za a binne da wadan nan kudade lokacin da ya zama bashi da amfani ga kowane sai dai abin daya aikata.
Sai dai duk da irin wannan son zuciya da kyashi da mungunta da masu manya da kananan kujerun suke nunawa alummominsu, Talaka bai taba nuna fushin sa ba, hasalima cewa yake Allah ya shirye su ya kuma kawo wasu nagari da zasu kwatanta adalci.
To yau she ‘Yan Najeriya zasu samu Shugabannin da zasu yi murna da zuwansu wadanda zasu yadda cewa Arzikin Najeriya yafi Al’ummarta yawa?.
Amma dai na san akwai lokaci da Talakawa zasu iya mayarwa da Kura aniyarta, nan da Dan lokaci.
Sai dai abin haushin har yan zu ana watsawa Dan adam Tsaba domin kawar da tunaninsa akan matakin da ya kamata ya dauka akan masu burin dauwama akan madafun ikon wanga kasa Mai albarka, wadda a kullum take kukan rashin tsayayyun mutane nagari masu kaunarta da burin kaita matakin koshi ba Yunwaba.
‘Yan Najeriya dai da hankalinsu kuma ba zasu kara yadda su yi gaban kan su ba wajen, jiran tsammanin da basu san lokacin tabbacinsa ba.
Nasan dai zuwa yanzu ‘Yan Najeriya sun haddace wakokin Zabiyar musan wajen cewa mun shirya sama muku Ruwan Sha da Lantarki da ilimi da hanyoyi da lafiya da Tattalin arziki da yaki da Talauci da Tsaro.
Jama’a duk wanda ya gaji da batun wakokin Zabiya a lokacin data ce “Durkusawa Wada da gajiyawa ce” , sai ya shiryar magance wan can matsala, da masu wanka da dukiyar Talaka suke sauyawa Salo ta hanyar lullube Kura da fatar Akuya.