


Daga NBA
Kungiyar matan Nigeria masu Rajin Kawo cigaba mai suna ‘Nigerian Women Progressive Alliance’ ta karrama kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma Alh. Hamza Safiyanu Kachako da matsayin Jakada zaman lafiya bisa kokarinsa na samar da aiyukan cigaban al’umma da tallafawa dalibai kuma matasa.
Da take mika Alamar karramawar Shugabar kungiyar Comrade Halima Musa ta ce sun karrama kwamishinan ne bisa la’akari da nagartartattun tsare tsarensa na bunkasa rayuwar al’umma ta fannoni daban da manufar Kara masa karfin guiwa akan haka.
Da yake karbar karramawar ta sabon Jakadan zaman lafiya
Ambasada Hamza Safiyanu Kachako ya ce hakan ya Kara masa kaimi wajen jajircewa akan aikinsa domin ganin gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ta cimma gagarumar nasara musamman wajen hidima ga al’ummar jahar kano da suka zabe ta.
Daga nan kwamishinan raya karkarar ya nemi hadin kai da goyon bayan al’ummar jahar kano domin cimma nasarar da aka sa gaba.