Dan Kirifto yace zai koma cin burodi da ruwa a gidan yari

Lauyan Sam Bankman-Fried, wanda ya samar da shafin kirifto na FTX – da ya rushe – ya ce Sam ya koma cin burodi da ruwa a gidan yari.

Gidan yarin – da aka ajiye shi yayin da ake ci gaba da yi masa shari’a – ba shi da abinci mai inganci da Mista Bankman-Fried ke buƙata, kamar yadda lauyan nasa ya bayyana.

A shekarar da ta gabata ne aka tuhume shi da laifuka bakwai da suka shafi zambatar mutane bayan da shafin kiriftonsa na FTX ya rushe.

A lokacin zaman kotun da aka gabatar ranar Talata Mista Bankman-Fried ya musanta aikata laifi kan tuhume-tume bakwai d ake yi masa .

Mista Bankman-Fried – wanda ake yi wa laƙabi da ”Sarkin Kirifto” – ya hallara gaban kotun ne sanye da kayan fursunoni

Lauyan tsohon biloniyan Mark Cohen, ya ce rashin wadataccen abinci a gidan yarin da Mista Bankman-Fried ke tsare na kawo tarnaƙi ga yadda suke shirya wa shari’ar, wadda aka tsara farawa cikin watan Octoba.

Mista Cohen ya kuma koka kan rashin samun wadatattun magungunan da biloniyan ke buƙata a gidan yarin.

Leave a Comment