An bukaci Al’umma su kai rahoton matsalar Ruwa ga sashin WASH dan daukar matakin gaggawa

Daga_NBA

Hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli a karkara ta jahar kano RUWASA ta bukaci al’ummar jihar da su kai rahoton matsalar ruwa da suke fuskanta ga sashen Ruwa da tsaftar muhalli ‘WASH’ dake kananan Hukumomin 44 domin daukar mataki na gaba.

Shugaban hukumar Alh. Shamwilu Abdulkadir Gezawa, ya bayyana haka a ganawarsa manema labarai a ofishinsa da ke Sharada anan birnin Kano.

Alh. Shamwilu Abdulkadir, ya ce Sashen WASH ne ke da alhakin tattara bayanai akan matsalolin tare da mika shi ga hukumar domin daukar matakin da ya dace.

Ya gargadi masu yada faifan bidiyo na karya kan amfani da gurbataccen ruwa da wasu al’ummomin karkara ke yi.

Shugaban Hukumar ta RUWASA wanda ya nuna nauyin da ya rataya a wuyan hukumar na samar da ruwa a inda babu ruwan famfo ya bayyana aikin hadin gwiwa da hukumar ke yi da kungiyoyi masu zaman kansu wajen gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da bandakuna a makarantu, da kasuwannni da cibiyoyin zamantakewa da horar da matasa akan gyaran rijiyoyin burtsatse.

Alh. Shamwilu Abdulkadir Gezawa, ya bada tabbacin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na samar da tsaftataccen ruwan sha da yaki da yin bahaya a waje a fadin jahar kano.

Leave a Comment