Alhazan Jihar Kano za su samu kyakykyawar kulawa a aikin Hajjin bana__DG Laminu Rabi’u

Daga Abubakar Sale Yakub

Darakta Janar na Hukumar jin da din alhazan Jihar Kano Alh, Laminu Rabi’u Danpappa, yayi alkawarin yin duk Mai yuwuwa wajen ganin  alhazan Jihar nan samu kulawar data dace a aikin Hajjin bana.

Alh. Laminu Danpappa ya bayyana hakan ne bayan ya karbi lambar yabo daga Ma’aikatan dake aiki a Asibitin  sansanin alhazai na Jihar Kano.

Ya bayyana jmgodiyarsa ga Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf, bisa kokarinsa wajen kyautatawa Alhazan Jihar Kano.

Ansa bangaren Shugaban Hukumar gudanarwa Hukumar Alhazan na Jiha, Alh Yusuf Lawan, yace Hukumar zata cigaba da bayar da dukkan taimakon da ya dace  Ma’aikatan bisa irin gudunmawar da suke bayarwa a loakcin aikin Hajj.

Ya Kuma yi kira a garesu dasu bayar da hadin Kai domin comma burin abin da aka Sanya a gaba.

Da yake jawabi tun dafari Jami’in dake kula da Asibitin sansanin alhazan Kuma Mataimakin Daraktan kula da Jami’an Jiyya a Hukumar kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Alh Ibrahim Abdullahi, yace sun zo Hukumar jin da din alhazai be domin gabatar da Lambar yabo ga Babban Daraktan bisa gwazonsa wajen tafiyar da  aiki, da kuma yadda aka kammala aikin jigilar alhazai a hajjin bana akan lokaci.

Da yake jawabi a loakcin taron Sheik  Isma’il Maccido, yace sunga lakuta uku na jagorancin Laminu Rabi’u kuma mutumne haziki Mai kwazo akan aikinsa.

Sheik Isma’il Maccido yayi Addu’ar Allah madaukakin Sarki ya kare shi ya kuma yi masa jangora, ya godewa Ma’aikatan Asibitin Sansanin alhazan Jihar Kano (Hajj Camp) bisa wannna lambar yabo da suka bashi.

Leave a Comment