HMB _ta kama mutumin da yake cutar marassa lafiya a Asibitin Yara na Hasiya Bayero-Dr. Nagoda

Hukumar kula da Manyan Asibitoci ta Jihar Kano ta kama wani mutum da yake sayarwa da marassa lafiya magani ba bisa ƙa’ida ba a Asibitin yara na Hasiya Bayero da ke cikin birnin Kano.

Shugaban Hukumar kula da Manyan Asibitoci ta Jihar Kano Dr. Mansur Nagoda, ya tabbatarwa da Wakilin Express Radio Abubakar Sale Yakub, kama mutumin, wanda yake sayarwa da marassa lafiya magani dan bata sunan gwamnatin Jiha.


Mansur Nagoda, yace dukkan magani da ake baiwa marassa lafiya a asibitin kyautane ba’a karbar kosisin kwabo.


Dr. Mansur Nagoda, yace a kokarin da suke na tabbatar da bin umarnin gwamnan Kano na bayar da maganida gwaje gwaje kyauta a asibitin Hasiya Bayero, sai sukai Kacibus da wanann mutum da yake sayar da magani a cikin asibitin.


Da yake jawabi game da wanann batu sabon Shugaban Asibitin Yara na Hasiya Bayero, Dr. Ibrahim Ibn Muhammad, yace tabbas sun kama mutumin kuma ba zasu saurara masa domin irin su ne suke batawa gwamnati Suna.


Shi kuwa Mutumin da aka kama yana sayar da magania cikin Asibitin Yara na Hasiya Bayero Yusuf Aminu Abdullahi, yayi karatun kula da lafiya, kuma ya tabbatar da cewa ya sayarwa da wani mutum allura, kuma ta ke ya sanya hannu cewa bashi ba asibitocin gwamnatin jiha.


Shugaban Hukumar kula da Asibitocin ta Jihar Kano Dr. Mansur Nagoda, ya kuma ja kunnen Maáikatan da aka turo Asibitin Hasiya Bayero dasu je aiki ko kuma sun kori kansu.


Tun dai lokacin da Gwamnatin Kano ta yiwa Asibitin Hasiya Bayero kwaskwarima dimbin jama’a suke turuwar zuwa asibitin harma wasu daga cikin iyayen marassa lafiya basa son fita daga asibitin duk kuwa da cewa an sallamesu sai an nusatar dasu suke fahimta sabo da yawan jama’a.

Leave a Comment