Hukumar alhazai ta Jihar da Majalisar dokokin Jiha zasuyi aiki tare dan inganta ayyukan Hukumar

Daga Abubakar Sale Yakub

Darakta Janar na Hukumar jin da din alhazai ta Jihar Kano Alhaji Laminu Rabi’u Danpappa, ya jaddada aniyarsa tayin aiki tare da Majalisar dokokin Jihar nan domin ciyar da ayyukan Hukumar Alhazai gaba.

Lamiru Rabi’u ya bayyana hakan ne a loakcin da yake karbar bakuncin Shugaban kwamitin aikin hajji na Majalisar dokokin yayin ziyarar da ya kai Hukumar.

Ya kara da cewa Hukumar jin da din alhazan zatayi iya yinta wajen hada hannu waje guda dan hindimatawa alhazai bisa gaskiya da amana.
Da yake nasa jawabin Shugaban kwamitin aikin hajji na Majalisar dokokin Jihar Kano Hon Sarki Aliyu Daneji, yace sun  ziyarci Hukumar ne domin sheda fuskokin mambobin kwamitin daga Majalisar dokokin Jihar Kano.
Hon Sarki Aliyu Daneji yayi kira ga Ma’aikatan Hukumar dasu bayar da hadin kai domin cimma burin da aka sanya a gaba.
Da yake jawabi Dan Majalisar Mai wakiltar Karamar Hukumar Dala a Majalisar dokokin Hon. Lawan Hussain Chediyar Yangurasa, ya shawarci Hukumar alhazan data tabbatar majiyatan da zasu gabatar da aikin Hajjin bana an basu isasshen lokacin domin su kammala shiri.
Ya kuma yi alkawarin taimakawa Hukumar wajen samar da dokokin Hukumar a Majalisar.
A nasa jawabi Shugaban Hukumar jin da din alhazan ta Jihar Kano, Alh Yusuf Lawan, yayi alkawarin yin duk Mai yuwuwa wajen ganin alhazai basu wahalaba a aikin Hajjin bana
Ya kuma godewa Kwamitin lura da aikin hajji na Majalisar dokokin Jihar Kano bisa ziyarar da suka kawo.

Leave a Comment