Maniyatan aikin hajji na Jihar Bauchi zasu fara ajiye naira miliyan uku

Daga Abubakar Sale Yakub

Hukumar jin da din alhazai ta Jihar Bauchi tace dukkan maniyacin aikin Hajjin 2024, zai fara ajiye Naira miliyan uku(3),


Babban Sakataren Hukumar Iman Abdurrahaman Ibrahim Idrsi ya bayyana haka yace Za a fara karbar kudin  a ranar 1st Ga wata Oktoba 2023,


A cewar Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar jin da din alhazai ta Jihar Bauchi.

Hukumar alhazai ta Jihar da Majalisar dokokin Jiha zasuyi aiki tare dan inganta ayyukan Hukumar

Daga Abubakar Sale Yakub

Darakta Janar na Hukumar jin da din alhazai ta Jihar Kano Alhaji Laminu Rabi’u Danpappa, ya jaddada aniyarsa tayin aiki tare da Majalisar dokokin Jihar nan domin ciyar da ayyukan Hukumar Alhazai gaba.

Lamiru Rabi’u ya bayyana hakan ne a loakcin da yake karbar bakuncin Shugaban kwamitin aikin hajji na Majalisar dokokin yayin ziyarar da ya kai Hukumar.

Ya kara da cewa Hukumar jin da din alhazan zatayi iya yinta wajen hada hannu waje guda dan hindimatawa alhazai bisa gaskiya da amana.
Da yake nasa jawabin Shugaban kwamitin aikin hajji na Majalisar dokokin Jihar Kano Hon Sarki Aliyu Daneji, yace sun  ziyarci Hukumar ne domin sheda fuskokin mambobin kwamitin daga Majalisar dokokin Jihar Kano.
Hon Sarki Aliyu Daneji yayi kira ga Ma’aikatan Hukumar dasu bayar da hadin kai domin cimma burin da aka sanya a gaba.
Da yake jawabi Dan Majalisar Mai wakiltar Karamar Hukumar Dala a Majalisar dokokin Hon. Lawan Hussain Chediyar Yangurasa, ya shawarci Hukumar alhazan data tabbatar majiyatan da zasu gabatar da aikin Hajjin bana an basu isasshen lokacin domin su kammala shiri.
Ya kuma yi alkawarin taimakawa Hukumar wajen samar da dokokin Hukumar a Majalisar.
A nasa jawabi Shugaban Hukumar jin da din alhazan ta Jihar Kano, Alh Yusuf Lawan, yayi alkawarin yin duk Mai yuwuwa wajen ganin alhazai basu wahalaba a aikin Hajjin bana
Ya kuma godewa Kwamitin lura da aikin hajji na Majalisar dokokin Jihar Kano bisa ziyarar da suka kawo.

HMB _ta kama mutumin da yake cutar marassa lafiya a Asibitin Yara na Hasiya Bayero-Dr. Nagoda

Hukumar kula da Manyan Asibitoci ta Jihar Kano ta kama wani mutum da yake sayarwa da marassa lafiya magani ba bisa ƙa’ida ba a Asibitin yara na Hasiya Bayero da ke cikin birnin Kano.

Shugaban Hukumar kula da Manyan Asibitoci ta Jihar Kano Dr. Mansur Nagoda, ya tabbatarwa da Wakilin Express Radio Abubakar Sale Yakub, kama mutumin, wanda yake sayarwa da marassa lafiya magani dan bata sunan gwamnatin Jiha.


Mansur Nagoda, yace dukkan magani da ake baiwa marassa lafiya a asibitin kyautane ba’a karbar kosisin kwabo.


Dr. Mansur Nagoda, yace a kokarin da suke na tabbatar da bin umarnin gwamnan Kano na bayar da maganida gwaje gwaje kyauta a asibitin Hasiya Bayero, sai sukai Kacibus da wanann mutum da yake sayar da magani a cikin asibitin.


Da yake jawabi game da wanann batu sabon Shugaban Asibitin Yara na Hasiya Bayero, Dr. Ibrahim Ibn Muhammad, yace tabbas sun kama mutumin kuma ba zasu saurara masa domin irin su ne suke batawa gwamnati Suna.


Shi kuwa Mutumin da aka kama yana sayar da magania cikin Asibitin Yara na Hasiya Bayero Yusuf Aminu Abdullahi, yayi karatun kula da lafiya, kuma ya tabbatar da cewa ya sayarwa da wani mutum allura, kuma ta ke ya sanya hannu cewa bashi ba asibitocin gwamnatin jiha.


Shugaban Hukumar kula da Asibitocin ta Jihar Kano Dr. Mansur Nagoda, ya kuma ja kunnen Maáikatan da aka turo Asibitin Hasiya Bayero dasu je aiki ko kuma sun kori kansu.


Tun dai lokacin da Gwamnatin Kano ta yiwa Asibitin Hasiya Bayero kwaskwarima dimbin jama’a suke turuwar zuwa asibitin harma wasu daga cikin iyayen marassa lafiya basa son fita daga asibitin duk kuwa da cewa an sallamesu sai an nusatar dasu suke fahimta sabo da yawan jama’a.

Alhazan Jihar Kano za su samu kyakykyawar kulawa a aikin Hajjin bana__DG Laminu Rabi’u

Daga Abubakar Sale Yakub

Darakta Janar na Hukumar jin da din alhazan Jihar Kano Alh, Laminu Rabi’u Danpappa, yayi alkawarin yin duk Mai yuwuwa wajen ganin  alhazan Jihar nan samu kulawar data dace a aikin Hajjin bana.

Alh. Laminu Danpappa ya bayyana hakan ne bayan ya karbi lambar yabo daga Ma’aikatan dake aiki a Asibitin  sansanin alhazai na Jihar Kano.

Ya bayyana jmgodiyarsa ga Gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf, bisa kokarinsa wajen kyautatawa Alhazan Jihar Kano.

Ansa bangaren Shugaban Hukumar gudanarwa Hukumar Alhazan na Jiha, Alh Yusuf Lawan, yace Hukumar zata cigaba da bayar da dukkan taimakon da ya dace  Ma’aikatan bisa irin gudunmawar da suke bayarwa a loakcin aikin Hajj.

Ya Kuma yi kira a garesu dasu bayar da hadin Kai domin comma burin abin da aka Sanya a gaba.

Da yake jawabi tun dafari Jami’in dake kula da Asibitin sansanin alhazan Kuma Mataimakin Daraktan kula da Jami’an Jiyya a Hukumar kula da Asibitoci ta Jihar Kano, Alh Ibrahim Abdullahi, yace sun zo Hukumar jin da din alhazai be domin gabatar da Lambar yabo ga Babban Daraktan bisa gwazonsa wajen tafiyar da  aiki, da kuma yadda aka kammala aikin jigilar alhazai a hajjin bana akan lokaci.

Da yake jawabi a loakcin taron Sheik  Isma’il Maccido, yace sunga lakuta uku na jagorancin Laminu Rabi’u kuma mutumne haziki Mai kwazo akan aikinsa.

Sheik Isma’il Maccido yayi Addu’ar Allah madaukakin Sarki ya kare shi ya kuma yi masa jangora, ya godewa Ma’aikatan Asibitin Sansanin alhazan Jihar Kano (Hajj Camp) bisa wannna lambar yabo da suka bashi.

An bukaci Al’umma su kai rahoton matsalar Ruwa ga sashin WASH dan daukar matakin gaggawa

Daga_NBA

Hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli a karkara ta jahar kano RUWASA ta bukaci al’ummar jihar da su kai rahoton matsalar ruwa da suke fuskanta ga sashen Ruwa da tsaftar muhalli ‘WASH’ dake kananan Hukumomin 44 domin daukar mataki na gaba.

Shugaban hukumar Alh. Shamwilu Abdulkadir Gezawa, ya bayyana haka a ganawarsa manema labarai a ofishinsa da ke Sharada anan birnin Kano.

Alh. Shamwilu Abdulkadir, ya ce Sashen WASH ne ke da alhakin tattara bayanai akan matsalolin tare da mika shi ga hukumar domin daukar matakin da ya dace.

Ya gargadi masu yada faifan bidiyo na karya kan amfani da gurbataccen ruwa da wasu al’ummomin karkara ke yi.

Shugaban Hukumar ta RUWASA wanda ya nuna nauyin da ya rataya a wuyan hukumar na samar da ruwa a inda babu ruwan famfo ya bayyana aikin hadin gwiwa da hukumar ke yi da kungiyoyi masu zaman kansu wajen gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da bandakuna a makarantu, da kasuwannni da cibiyoyin zamantakewa da horar da matasa akan gyaran rijiyoyin burtsatse.

Alh. Shamwilu Abdulkadir Gezawa, ya bada tabbacin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na samar da tsaftataccen ruwan sha da yaki da yin bahaya a waje a fadin jahar kano.

Shin Matasan Arewa zasu iya kawo sauyi tabangaren Shugabaci a Najeriya?

Daga Abubakar Sale Yakub

Rayuwarku matasa tana da muhammaci ga cigaban Kasa dan suke shiga cikin aikata laifukane?


An ya kuwa Idan aka tafi a haka zaku iya Jan ragamar al’ummar Najeriya kuwa? gaskiya da sake, Idan aka tafi a haka matasa ba zasu taba janragar al’ummar kasarnan ba mutukar baku dai shaye shaye ba.


Ku sani akwai kasashen Duniya da dama da suka jaraba matasa kuma sun sami abin da suke bukata.


Amma haka suka zauna suna aikata laifuka? da shaye shaye? Amsar itace aa,

Domin sunyi karatu kuma iyayensu ba wasu bane duk fa suna kasashen da babu ruwansu da addini basa aikata laifuka.

Dan haka matasan Najeriya zaku iya cin moriyar Damar da aka baku ta shugabantar jama’a matsawar kunyi ilimi kun kuma kaucewa shaye shayen miyagun kwayoyi wanda shine yake lalata rayuwar matasanmu musamman nan Yankin Arewa kususan Jihar Kano.


Shawara Gareku itace kada kuyarda da hudubar Manya ‘yan siyasa na cewar zaku karesu sabi da bukatar Kansu, Rahotanni na nuni da cewa baragurbin ‘Yan siyasa sun tanadi kayan fada sabo daku to kada kukuskura kubi su, Idan gaskiya ne suka hadaku da ‘Ya yansu.

Da wannan nake cewar gyara kayanka bai taba zama sauke muraba ba Muhadu a rubuta na gaba.

Dan Kirifto yace zai koma cin burodi da ruwa a gidan yari

Lauyan Sam Bankman-Fried, wanda ya samar da shafin kirifto na FTX – da ya rushe – ya ce Sam ya koma cin burodi da ruwa a gidan yari.

Gidan yarin – da aka ajiye shi yayin da ake ci gaba da yi masa shari’a – ba shi da abinci mai inganci da Mista Bankman-Fried ke buƙata, kamar yadda lauyan nasa ya bayyana.

A shekarar da ta gabata ne aka tuhume shi da laifuka bakwai da suka shafi zambatar mutane bayan da shafin kiriftonsa na FTX ya rushe.

A lokacin zaman kotun da aka gabatar ranar Talata Mista Bankman-Fried ya musanta aikata laifi kan tuhume-tume bakwai d ake yi masa .

Mista Bankman-Fried – wanda ake yi wa laƙabi da ”Sarkin Kirifto” – ya hallara gaban kotun ne sanye da kayan fursunoni

Lauyan tsohon biloniyan Mark Cohen, ya ce rashin wadataccen abinci a gidan yarin da Mista Bankman-Fried ke tsare na kawo tarnaƙi ga yadda suke shirya wa shari’ar, wadda aka tsara farawa cikin watan Octoba.

Mista Cohen ya kuma koka kan rashin samun wadatattun magungunan da biloniyan ke buƙata a gidan yarin.

Kungiyar NIWOPA ta Karrama Kwamishina Kachako da Ambasadan Zaman lafiya

Daga NBA

Kungiyar matan Nigeria masu Rajin Kawo cigaba mai suna ‘Nigerian Women Progressive Alliance’ ta karrama kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma Alh. Hamza Safiyanu Kachako da matsayin Jakada zaman lafiya bisa kokarinsa na samar da aiyukan cigaban al’umma da tallafawa dalibai kuma matasa.

Da take mika Alamar karramawar Shugabar kungiyar Comrade Halima Musa ta ce sun karrama kwamishinan ne bisa la’akari da nagartartattun tsare tsarensa na bunkasa rayuwar al’umma ta fannoni daban da manufar Kara masa karfin guiwa akan haka.

Da yake karbar karramawar ta sabon Jakadan zaman lafiya
Ambasada Hamza Safiyanu Kachako ya ce hakan ya Kara masa kaimi wajen jajircewa akan aikinsa domin ganin gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ta cimma gagarumar nasara musamman wajen hidima ga al’ummar jahar kano da suka zabe ta.

Daga nan kwamishinan raya karkarar ya nemi hadin kai da goyon bayan al’ummar jahar kano domin cimma nasarar da aka sa gaba.

Har yanzu ba ta sauya zani ba a Najeriya

Daga Abubakar Sale Yakub

Talaka ya kwana ya tashi bai ci ba, sabo da karfin hali haka zai sake fita   nema a taskar Allah.

Yayin  da wanga wadan cha nan ka suke haka Rami su binne na Gwamna masu gida rana (Kudi)  Dan gudun talauci.

Wannan rayuwa ta munana amma dai nasan tabbas babu wanda za a binne da wadan nan kudade lokacin da ya zama bashi da amfani ga kowane sai dai abin daya aikata.

Sai dai duk da irin wannan son zuciya da kyashi da mungunta da masu manya da kananan kujerun suke nunawa alummominsu, Talaka bai taba nuna fushin sa ba, hasalima cewa yake Allah ya shirye su ya kuma kawo  wasu nagari da zasu kwatanta adalci.

To yau she ‘Yan Najeriya zasu samu Shugabannin da  zasu yi murna da zuwansu wadanda zasu yadda cewa Arzikin Najeriya yafi Al’ummarta yawa?.

Amma dai na san akwai lokaci da Talakawa zasu iya mayarwa da Kura aniyarta, nan da Dan lokaci.

Sai dai abin haushin har yan zu ana watsawa Dan adam Tsaba domin kawar da tunaninsa akan matakin da ya kamata ya dauka akan masu burin dauwama akan madafun ikon  wanga kasa Mai albarka, wadda a kullum take kukan rashin tsayayyun mutane nagari masu kaunarta da burin kaita matakin koshi ba Yunwaba.

‘Yan Najeriya dai da hankalinsu kuma ba zasu kara yadda su yi gaban kan su ba wajen, jiran tsammanin da basu san lokacin tabbacinsa ba.

Nasan dai zuwa yanzu ‘Yan Najeriya sun haddace wakokin Zabiyar musan wajen cewa mun shirya sama muku  Ruwan Sha  da  Lantarki da ilimi da hanyoyi da lafiya da Tattalin arziki da yaki da Talauci da Tsaro.

Jama’a duk wanda ya gaji da batun wakokin Zabiya a lokacin data   ce  “Durkusawa Wada da gajiyawa ce” , sai ya shiryar magance wan can matsala, da masu wanka da dukiyar Talaka suke sauyawa Salo  ta hanyar lullube Kura da fatar Akuya.

Yan Nijar Mazauna Kano sun bukaci a dawo da Bazoum kan kujerarsa

Wasu Yan Kasar Niger Mazauna Jihar Kano sun gudanar da Zanga Zangar lumana ta nuna rashin goyon bayan juyin Mulkin da sojoji sukayi a Kasar.

Masu zanga Zangar sunyi kira da a mayar da Muhammad Bazoum Kujerarsa batare da bata lokaci ba.

Sun kuma ja hankalin kungiyar Cigaban Tattalin Arziki kasashen Afrika ta yamma ECOWAS data gudanar da aikinta cikin lumana dan ganin an dawo da Bazoum kujerar Shugabancin Kasar Niger.