Hukumar NDLEA ta kama dalolin Amurika na jabu

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta ce jami’anta sun kama dalar Amurka miliyan 20 ta jabu.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta yi kamen ne a kan hanyar Abaji zuwa Lokoja a Abuja, babban birnin Najeriya.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya tabbatar da cewa an samu kudin na jabu a cikin wata mota wadda ta taso daga Legas zuwa Abuja.

Mista Babafemi ya bayyana cewa an kama direban motar mai shekara 53.

NDLEA ta ce kwana guda kafin ta kama dalolin da take zargin na bogi ne, sai da ta kama wani mutum mai shekara 52 da kilo 2.2 na kwayar methamphetamine a wani samame da jami’an hukumar suka kai a kauyen Kabusa da ke Abuja.

Hukumar ta ce tun da farko ta kama mutumin da take zargi da kilo 20.75 na tabar wiwi a ranar 7 ga watan Yulin 2022, inda kotu ta bayar da belinsa, a yayin haka ne aka soma kama shi kan zargin wani laifin.

Haka kuma, NDLEA din ta kai wani samame a matattarar ’yan shaye-shaye biyu a unguwannin Dei Dei da Tora-Bora da ke Abuja, inda aka gano kilo 1.8 na rohypnol da kilo 1.2 na diazepam a ranar Laraba 16 ga watan Agusta.

Gwamnatin Jihar Kano za ta raba kayan aikin Gayya ga Kungiyoyi

Gwamnatin jahar kano za ta samar da wadataccen kayan aiki ga kungiyoyin aikin gayya domin yashe magudanun Ruwa.

Kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma Alh. Hamza Safiyanu Kachako ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kwamitin koli na aikin gayya a ofishinsa dake ma’aikatar.

Alh. Hamza Safiyanu Kachako wanda ya bayyana muhimmancin kwamitin ga al’umma ya ce samar da kayan aikin zai karawa kungiyoyin karfin guiwa domin cigaba da jajircewa wajen yashe magudanun Ruwa akai akai.

A nasa jawabin shugaban kwamitin Comrade Aminu Garba Kofar Na’isa ya ce sun ziyarci kwamishinan ne domin taya shi murnar nada shi a matsayin sabon kwamishinan ma’aikatar tare da jaddada kudirin kwamitin na goyon bayan manufofin gwamnati na tallafawa al’umma.

Kazalika, kwamishinan ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma Alh. Hamza Safiyanu Kachako ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar cigaban matasan garin Kachako KAYDA bisa jagorancin Comrade Rabi’u Sale Damina da Mustafa Aliyu Kachako.

Shugabannin sun ce ziyarci kwamishinan ne domin taya shi murna da ba shi shawarwari da kuma yin addu’o’i alkhairi domin samun nasara a nauyin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora masa na jagorancin ma’aikatar.

Gwamnatin Kano tace zata cigaba da wayar da kan Jama’a yadda zasu yi amfani da gidan sauro

Gwamnatin Kano jihar Kano tace ta himmatu wajen cigaba da wayar da akan jama’a game da muhimmancin amfani da gidan sauro.

Kwamishinan lafiya na Jiha Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa , ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wajen rufe taron gangamin rabon gidajen sauro a fadin Jihar Kano.

Dr. Tsanyawa, yace gangamin rabon gidajen sauron yazo da kalubale iri iri, sai dai bisa taimakon Allah an aiwatar da aikin bisa kokarin gwamnatin Kano da sauran abokan huldarta sun gudanar da aikin rabon gidajen sauron na shekarar 2022 kamar yadda aka tsara.

Manajan shirin rabon gidan sauron a jihar Kano Dr. Abdullahi Isa Kauranmata, kwamishinan ya godewa aniyar Asusun Global Fund, bisa kokarinsa na sanya kudade masu waya wajen inga lafiya da kuma baiwa alummar Jihar Kano kulawar data dace.

Ya kuma yabawa kokarin abokan hulda musamman kungiyoyin da suke cikin shirin, sabo da yadda suka kwashe tsahon kwanaki suna ta kokarin ganin aikin ya tafi dai dai.

Da yake nasa jawabin John Ocholi daga kungiyar kula da lafiyar iyali yace aikin gangamin rabon gidajen sauro a jihar Kano ya samu gagarumar nasara, ya kuma godewa Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, bisa kokarinsu ga alummar Jihar Kano.